Waɗanda su ka yi garkuwa da Hanifah Abubakar, ƴar shekara 5 a Jihar Kano, sun kashe ta duk da sun karɓi wani abu da ga cikin naira miliyan 6 da su ka nemi a basu a matsayin kuɗin fansa.


Baffan ta, Suraj Suleman ne ya tabbatar da kisan nata da kuma gano sassan jikin ta a wata tsohuwar makarantar kudi a unguwar Tudunwada a Kano.
A cewar sa, da farko, wanda yai garkuwa da Hanifah, ya kai wajen matar sa, amma sai ta ƙi ta karɓe ta.
“Da ga nan ne sai ya kaita Tudunwada inda ya ke da wata makarantar kuɗi. Sai ya haɗa mata shayi da shinkafar ɓera a ciki ta sha.
“Bayan ta sha shayin, sai ta mutu. Da ga nan sai wanda yai garkuwar da ita ya daddatsa jikin ta ya binne ta a cikin makarantar,” in ji baffan nata.
Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa an kama wadanda su ka yi garkuwa da Hanifah ne a wajen titin Zariya a jiya daddare lokacin da su ke ƙoƙarin karɓar cikin kuɗin fansar.
A tuna cewa tun a ranar 4 ga watan Disambar 2021 ne masu garkuwa da mutane su ka ɗauke Hanifah bayan da su ka zo a adaidaita-sahu su ka yaudare ta su ka sungume ta