Home Labarai
0

 ‘Yan Sanda Dun Kuɓutar Da Wani Matashi Da Aka Kusa Yi Wa Yankan Rago A Kano.

Rundunar Ƴan Sanda a Jihar Kano ta ce ta kuɓutar da wani matashi da a ke zargin wasu ƴan damfara sun yi yunƙurin yi wa yankan rago, kamar yadda BBC ta rawaito.

Lamarin ya faru ne a wani gida a Ƙaramar Hukumar Dambatta a Kano. Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, DSP Abdullahi Kiyawa, ya shaida wa BBC cewa: 

“Mun sami labarin faruwar lamarin ne bayan da matashin da aka fara yankawa maƙogwaro ya kai musu ƙorafi, an take mu ka garzaya da shi asibiti”.

Matashin, mai shekara 23, ya baiyana wa BBC cewa a dandalin sada zumunta na Facebook su ka haɗu da wanda ake zargi da yunƙurin halaka shi.

Ko a makon da ya gabata ma an kama wani matashi da ya yi wa wata yarinya ‘yar makotansu yankan rago a karamar hukumar Tofa a Kano, bayan ya nemi kudin fansa daga wajen iyayenta.

READ ALSO:  Ina neman matar Aure – IBB

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here