Home Labarai Alkawurra 14 da Buhari ya yi wa ‘yan Najeriya a 2020

Alkawurra 14 da Buhari ya yi wa ‘yan Najeriya a 2020

0

Hakkin mallakar hotoBUHARI SALLAU

A sakon shiga sabuwar shekarar 2020 da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi ta gidan talbijin din kasar, ya lissafo manyan ayyukan da yake sa ran zai yi a shekarar.

Muhimman ayyukan da shugaban ya ce zai yi a sabuwar shekarar sun hada da:

Tituna 47 da za a yi a tsakanin 2020/21 da suka hada da hanyoyin da suka dangana ga tashoshin ruwa.

Inganta jami’an tsaro ta hanyar sama musu kayan aiki na zamani da bai wa sojojin horo.

Manyan gadoji musamman gadar Second Niger Bridge.

Kammala ayyukan rukunin gidaje 13 karkashin tsarin samar da gidaje na kasa.

Kaddamar da filayen jirgin sama a Lagos da Kano da Maiduguri da Enugu a 2020.

Kaddamar da shirin aikin gona a karkara a kananan hukumomi 700 a tsawon shekaru uku.

Horas da ma’aikata 50,000 domin taimaka wa malaman gona 7,000 da ake da su.

Kaddamar da shirin gandun kiwon dabbobi a Gombe.

Kaddamar da titin jirgin kasa na Lagos zuwa Ibadan da Itakpe zuwa Warri a watanni ukun farkon 2020.

Fara aikin hanyar jirgin kasa da za ta tashi daga Ibadan zuwa Abuja da kuma Kano zuwa Kaduna a farkon watannin ukun 2020.

Kara sakar wa harkar wutar lantarki mara domin bai wa masu sanya hannun jari damar samo da sayar da wutar lantarki.

Gwamnatin tarayya za ta horas da malaman gona 50,000 wadanda za su zama kari ga 7,000 da ake da su a kasa.

Fara aikin ginin tashar wutar lantarki ta Mambilla a watannin shidan farkon 2020.

Fara aikin jan bututun iskar gas AKK gas pipeline, da OB3 gas pipeline da kuma fadada bututun iskar gas din na Escravos zuwa Lagos a watanni ukun farko na 2020

READ ALSO:  Shekaru 70 Na Gwamna Abdullahi Umar Ganduje: Me Ka Sani Game Da Shi?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here