Gareth Bale, dan wasan Real Madrid. REUTERS/Andrea Comas
Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya nuna yana so a gaggauta sayar da dan wasan gaba da kungiyar ta saya da tsada daga Tottenham Gareth Bale a wannan kaka.
Dangantaka tsakanin mutanen biyu dai ta yi tsami fiye da kima, inda har ta ruguje, har ma ya kasance kungiyar ba ta da wani zabi illa ta sayar da dan wasan.
Sai dai babu wani wanda ya taya wannan dan wasa, ko ya nuna sha’awa a hukumance.
A kwanan nan ma dan wasan ya shaida wa manema labarai cewa yana bukatar barin Real Madrid amma kungiyar tana mai kafar ungulu a al’amarin barin nata.
A ranar daya ga watan Satumban shekarar 2013 ne Bale ya baro Tottenham zuwa Real Madrid a kan kudin da aka yi amannar ya kai Yuro miliyan 91.