Home Kannywood Dandalin Kannywood: Zahraddeen Sani Ya Baza ‘Yan Sanda Neman Ummi Zee Zee...

Dandalin Kannywood: Zahraddeen Sani Ya Baza ‘Yan Sanda Neman Ummi Zee Zee Ruwa A Jallo.

0

Dandalin Kannywood: Zahraddeen Sani Ya Baza ‘Yan Sanda Neman Ummi Zee Zee Ruwa A Jallo.

A Yanzu haka rundunar ‘yansandan Nijeriya na farautar tsohuwar jarumar fina finan kannywood Umme zee zee sakamakon kararta da shahararen jarumin kannywood Zahrraddeen Sani ya shigar saboda tuhumarta da yake da yunkurin bata masa suna.

Jaridar Premium Times ta ruwaito makasudin wannan rikice shine zee zee ta zargi wasu ‘yan  film da suka hada da Zahraddeen Sani,Sani Danja,Fati Muhammed,Al’ameen Buhari,Yakubu Muhammed,Da Imrana Muhammed da wareta alokacin da suka gana da wakilan Atiku Abubakar a kaduna.

Zahraddeen Sani ya bayyana cewa Zee Zee bata da masaniya game da taron,su suka shirya abin su batare da sun sanyata ciki ba,kuma sun bayyana wakilan Atiku Abubakar irin gudunmuwar da suke bashi a matsayin su na taurarin Kannywood.

Alokacin da Zee Zee ta samu labarin taron,sai ta nemi aboka nan aikinta dasu bata nata kason alherin da suka samo daga taron,wanda jagoran yakin neman zaben Atiku,shugaban majakisar dattawa sanata Bukola Saraki ya halarta.

Kammala wannan taro keda wuya sai Zee Zee ta buga a shafinta na Instagram tana zarginsu Zahraddeen Sani da yaudararta,har tana kiransu barayihar ma tayi barazanar daure dukkansu,inda take bugun kirji cewa duk ta fisu sanin manya a Nijeriya.

“Ina da labarin Atiku ya aiko mana da makudan kudade,amma da yake ku barayi sai kuka rabe kudin a tsakaninku,wallahi da badon mahafiyata ta bani hakuri ba,da saina daureku gaba daya,ai gashi bayan taron Zahraddeen Sani ya aiko min da N25,000,kai kasani nifa ba mabaraciya bace,daga yau sai yau idan kuka sake min irin haka saina yi maganinku.Inji ta”

READ ALSO:  ango suka daga amarya sama wai sabi da dadin shagalin biki

Sai dai Zahraddeen Sani ya tabbatarwa manema labarai cewa N25,000 daya baiwa Zee Zee kyauta ne daga aljihunsa,saboda a cewarta bada ita suka shirya taron ba,kuma bata da wata gudunmuwa da zata basu saboda batada sauran tasiri a Kannywood.

“Ina so ka sani cewa yanzu na shigar da kararta gaban jukumar ‘yan sanda a kaduna,kuma tuni suka shiga nemanta ruwa a jallo,na kai kararta ne saboda ta zargeni ni da abokaina akan tafka laifin sata,wai mun kwashe kudin da Atiku ya bamu,Inji Shi.”

Zuwa yanzu ta bayyana cewa akwai magoya bayan takarar shugaban kasa Muhammad Buhari kuma akwai masu goyon bayan Atiku Abubakar,wasu da cikin magoya bayan Buhari sun hada da Ali Nuhu,Adam Zango,Rabi’u Rikadawa da dai sauran su.

   

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here