Home Labarai Iran ta yi Allah wadai da kisan Soleiman

Iran ta yi Allah wadai da kisan Soleiman

0

Iran ta yi Allah wadai da kisan Soleiman

Daga Zulaiha Abubakar

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta yi Allah wadai da harin da Amirka ta kai filin jirin sama na birnin Bagadaza, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar kwamanda Qasem Soleiman jagoran dakarun juyin juya hali a yau Juma’a

Shugaban kasar Amirka Donald Trump ya sanar da bayar da umarnin kashe kwamanda Qasem Soleiman jagoran dakarun juyin juya hali na kasar Iran cikin wata sanarwa da  cibiyar tsaro ta Pentagon ta fitar a wannan Juma’ar.

Sanarwar ta kara da bayyana cewar, daukar wannan mataki ya zamarwa Amirka tilas saboda kare rayuwar jami’anta da ke kasashen ketare. Shugaba Trump ya bayyana yadda kwamandan da mataimakansa suke shirin kaiwa wakilan huldar jakadancin Amirka da ke aiki a Iraki da sauran bangarori farmaki, ya kuma kara da dora alhakin harin da masu zanga-zanga suka kaiwa ofishin jakadancin Amirka a birnin na Bagadaza cikin wannan mako akan kwamandan na dakarun juyin juya halin na kasar Iran.

Tuni da gwamanatin ta Iran ta bakin shugaban kasar Hassan Rouhani ta bayyana cewar za ta mayar da martani kakkausa kan kisan Soleiman din wanda Amirka ta dau alhakin yi

READ ALSO:  Pantami Ya kara Gina Katafaren Masallaci a cikin Makaratar GSSS Gombe

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here