Home Labarai jana’izar shibuhuhar yan kogo

jana’izar shibuhuhar yan kogo

0

 

JANA’IZAR SHUBUHAR ƳAN KOGO, AKAN HANA ABDULJABBAR YIN AMFANI DA LITTAFI MAI SHARHI A KOTU…

Bayan an tashi daga kotu jiya, mun kawo sahihin rahoto akan abubuwan da suka faru a kotun, kuma a ciki muka ambata muku cewa Abduljabbar ya dauko littafin Sahihu Muslim mai sharhi yana magana a kansa. Kuma an dakatar da shi, anyi masa umarnin ya dauko zallar matanin Muslim din, inda yace ba shi da shi, har aka daga shari’ar akan zama na gaba za’a kawo littafin.

Tun da muka saki wanda rahoton, yaran Abduljabbar suka dauki waccan gabar da na ambata a sama, suka dinga kawo sharri da shubuhohi iri-iri domin nuna gazawar mu. Har ma wasun su da yawa suka dinga tambaya ta dalili akan hakan.

A wannan rubutun, zan fayyace musu yadda abin yake, kuma idan har gaskiya suke nema, zasu samu waraka daga shubuhar tasu.

GABA TA FARKO, BATUN SHAIDU…

A wannan shari’ar, masu gabatar da ƙara suna da shaidu guda iri biyu ne:

i: Shaidugani da ido: Su wadannan, shaidu ne da zasu tabbatarwa da kotu cewa sun ji da kunnen su, Abduljabbar ya fadi wadannan kalmomi da ake tuhumar sa akan su. A gabansu ya faɗa, ba labari aka basu ba.

ii. Professionals: Su kuma wadannan, masana ne, kwararru akan fannin da ake shari’ar a kai, su kuma shaidar su zata kansance ne akan ma’anoni da abinda kalaman suke nufi, ko kuma zurfafa magana a kan fannin ilimi.

To gaɓar da ake ciki yanzu haka a kotu, ana sauraron shaidu ne wadanda suka ji abubuwan da Abduljabbar ya faɗa da bakin sa. Ba azo bayani akan wadansu ma’anoni ba.

Jigon abinda shaidun suke bayar da shaidar su a kai shine: Ni wane, a ranar … ga watan…, naji Abduljabbar ya fadi abu kaza, kuma yace a cikin Bukhari/Muslim aka fadi hakan, kuma ya fadi lambar hadisi, kuma na duba lambar da ya faɗa ban gani ba. Kuma wannan abin da na fada, a gaba na aka yi, ba labari aka bani ba….

READ ALSO:  Tirkashi: Kungiyoyi sun bukaci a bar karuwai su fara rijista a Najeriya

To duk wanda ya san menene Shari’a, idan ya tashi zai yi tambayoyi ga irin wannan shaida, zai yi masa ne a iyaka abinda ya faɗa, ba zai fita daga wannan ba.

GABA TA BIYU: ABDULJABBAR DA LAUYOYINSA

A bangaren Abduljabbar da lauyoyin sa, suna da damarmaki guda uku a shari’ar:

i. Abduljabbar ko lauyoyin sa, suna da damar yin tambayoyi ga shaida, abinda ake kira CROSS EXAMINATION, domin su rusa shaidar da ya bayar. A nan, suna da damar gabatar da littafin da shaida ya ambata, domin su tabbatar da abin da ya kore, ko su kore abinda ya tabbatar. A takaice ce dai, iyaka abubuwan da shaida ya faɗa zasu yi ƙoƙarin rusawa, A nan, ba wuri ne na bayani ba, wuri ne na tambaya da masa tsakanin wanda ake ƙara ko lauyansa da kuma shaida.

ii. Bayan Abduljabbar ko lauyoyin sa sun gama yiwa shaida tambayoyi, suna da damar yin suka akan shaidar, misali suce ‘Ya mai shari’a, muna rokon wannan kotu tayi watsi da wannan shaidar da wane ya bayar, saboda yace nayi abu kaza, amma ya tabbata bashi da hujja, yace na fadi magana, ya duba a Muslim kuma bai gani ba, amma gashi na nuna wajen a Muslim din” da sauran su. A nan, shaida ba shi da damar magana, damar sa ta kare a baya, yanzu hukunci kotu zata yi akan karba ko watsi da shaidar da aka gabatar din.

iii. Idan an gama sauraron shaidu akan sun tabbatar sun ji Abduljabbar ya fadi kalmomin da ake tuhumar sa akansu, dole akwai matsaya, ya faɗa, ko bai fada ba?

READ ALSO:  Shekaru 70 Na Gwamna Abdullahi Umar Ganduje: Me Ka Sani Game Da Shi?

Wannan amsar tana da muhimmanci sosai, amma alƙali baya fadinta sai a hukunci na karshe.

To a nan ake bawa wanda ake ƙara cikakkiyar dama ya kare kan sa daga abinda ake tuhumar sa. wannan itace damar Abduljabbar ta uku, ita ake kira DEFENCE, a lokacin da Abduljabbar zai yi defence, yana da damar yin amfani da kowanne irin littafi yaga dama domin ya kare kansa. Kuma yana da hakkin a ba shi cikkaken lokaci da zai kare kansa, ba tare da an katse shi ba har sai yace ya kammala. Kuma a wannan gaɓar ne masu gabatar da kara zasu iya gabatar da Shaidu nau’i na biyu, wato Professionals, domin suyi magana akan ma’anonin da Abduljabbar ya fada.

Idan kun fahimci rubutu na tun daga farko har zuwa nan, zaku gane cewa:

1. A yanzu shaidar gani da ji ake gabatarwa, ba kwararru a fannin ilimi ba.

2. A yanzu iyakar damar Abduljabbar itace ya ƙaryata shaida akan ko baiji karatun Abduljabbar din ba, ko labari aka ba shi, ko ya manta abinda ya faɗa, ko karya yake masa bai fada ba. Ba wani bayani na daban ake so yayi ba. Wato Cross Examination zai yi ba Defence ba.

3. Abinda yasa aka hana Abduljabbar yin amfani da Sharhin Muslim shine, a karatun sa, ya ambaci Littafin Muslim ne ba sharhin sa ba, kuma shima shaida Muslim yaje ya duba, kuma Muslim fadawa kotu ya duba ba sharhin sa ba. Toh dole Abduljabbar Muslim zai gabatar ba sharhin ba.

GABA TA UKU: ALBISHIR

Da ace ma ƴan Kogo zasu kwantar da hankalin su, alƙali ya yiwa Abduljabbar alkawura guda uku:

READ ALSO:  TARAIRAYA MAGANIN RIKICIN GIDAN AURE

i. Zai bashi damar zuwa da ko wadanne irin littattafai ko sun kai Mota nawa, idan lokacin hakan ya zo. (Duk da yake yanzun ma yana zuwa da su kuma ba’a hana shi ba, a zama na shida, yazo da littafi guda 13, a zama na bakwai ya zo da guda 35, a zaman jiya kuma yazo da guda 124 kamar yadda na ƙirga).

ii. Zai ba shi damar kare kan sa, ko da za’a dinga zama daga 9 na safe har zuwa la’asar, idan yana kare kan nasa.

iii. Idan lokacin haka yayi, koda wani abu yake so ya kunna na AUDIO, za’a ba shi dama. (Tun da ai jiyan ba iyaka Sharhi aka hana yayi amfani da shi ba, yazo da KATUWAR MP3 wai zai kunna murya, aka ce ya bari sai anzo gaɓar tukunna).

Ina fatan duk wanda ya karanta wannan bayanin da wankakkiyar zuciya, zai samu waraka daga kowacce irin fahimta mara kyau akan ma’asalar.

Da wannan nake rokon Allah ya karawa wannan shubuhar nauyin ƙasa, domin tabbas ta mutu.

Kuma ina kalubalantar Jilani Makwarari, da Prince Hafiz da suka matsa akan nayi bayani in dai akwai gaskiya a lamarin, to ga shi nayi, In kun isa su warware abin da na fada da hujja mai karfi irin tawa. (Titsiye Mode Activated)…

Allah Ya bamu ikon sanin gaskiya tare da aiki da ita.

Awaisu Al’arabee Fagge

Jibwis Social Media

Kano State.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here