Majalisar Dattawa Da Ta Wakilai Sun Miƙa Wuya Ga Buƙatar Shugaba Buhari Ta Yin Sauyin Dokar Zaɓen
Majalisar dokokin Najeriya ta yi wa kudurin dokar zabe gyaran fuska, inda a yanzu ‘yan majalisun suka ba wa jam’iyyun siyasa damar zabar tsarin da suke so wajen fitar da ‘yan takara.
A bisa gyaran da majalisun biyu ta dattawa da kuma ta wakilai suka yi, a yanzu kudurin ya tanadi cewa kowace jam’iyya za ta iya fitar da ‘yan takararta ta hanyar zabar ‘yar tinke ko kai tsaye ko kuma ta sasanto.
A da majalisun sun zartar da cewa kowace jam’iyya za ta rika fitar da ‘yan takararta ne ta hanyar zaben ‘yar tinke kawai.
Bayan an mika wa Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya sanya hanu a kan kudurin domin ya zama doka sai ya ki amincewa da wannan tsari, yana bukatar su bayar da wani zabi, abin da ya sa aka maida wa hadakar majalisar kudurin inda ta sake bibiyar kudurin a yanzu tare da yin kwaskwarimar, kamar yadda BBC Hausa ta rawaito.
A yayin zaman da suka yi ne daban-daban a ranar Larabar nan, aka sake gabatar da kudurin, inda Sanata Yahaya Abdullahi ya gabatar da shi a majalisar dattawa yayin da Abubakar Fulata ya gabatar a majalisar wakilai.