Home Labarai Ruwan sama ya fara kashe wutar dake cin Australiya, kwana 1 bayan...

Ruwan sama ya fara kashe wutar dake cin Australiya, kwana 1 bayan addu’ar Musulman kasar

0

Ruwan sama ya fara kashe wutar dake cin Australiya, kwana 1 bayan addu’ar Musulman kasar

Kwana 1 bayan addu’ar Musulmai, ruwan sama ya fara kashe wutar dake cin Australiya

DABO FM ta binciko cewar cikin kasa da kwana 1 da Musulman kasar Australiya suka fito domin yin addu’ar rokon ruwan sama, ruwan saman ya sauko, ya fara cin wutar da take cin dazukan kasar.

Tin dai ranar 20 ga watan Disambar 2019, wata wuta ta fara ci a wani dajin dake arewa maso gabashin kasar wanda ta yadu ya kai ga tashi adadin ma’aunin filaye 15,000.

A ranar 6 ga watan Janairun 2020, musulman kasar suka taru a wani lambun rage gajiya na Bonython Park dake birnin Adelaide, babban birnin jihar Kudancin Australiya.

Musulman sama da 50 sun taru domin yin addu’ar samun ruwan sama ko wutar data shafe makonni tana ci duk da irin aiki da hukumar kashe gobarar kasar takeyi na kashe wutar ta hanyar amfani da hanyoyin zamani, kamar yacce Jaridar Daily Mail ta kasar Ingila ta tabbtar.

DABO FM ta tattaro cewa a yau, 6 watan Janairun 2020, ruwan sama ya sauka cikin kasar, ya kuma fara kashe wutar data dade tana ci a dajikan kasar ta Australiya.

BBC ta rawaito cewar ruwan ya fara ne sauka ne daga gabar bakin tekun gabashin kasar, daga birnin Sydney har zuwa Melbourne tare da rahotannin fara samun haduwar hadari da tsawa a wasu bangarorin New South Wales.

READ ALSO:  Wani Bakanike Yayi Ma Uwa Da Yayanta Mata Guda Biyu Cikin Shege

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here