Home Labarai Sheikh Bala Lau ya yi jimamin rasuwar Ibrahim Abdul’aziz na Muryar Amurka

Sheikh Bala Lau ya yi jimamin rasuwar Ibrahim Abdul’aziz na Muryar Amurka

1

Shugaban kungiyar JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau a madadin kungiyar ta Islama, ya yi matukar juyayin rasuwar wakilin sashen Hausa na Muryar Amurka a jihar Adamawa da Taraba Ibrahim Abdul’aziz a sanadiyyar hatsarin mota kan hanyar Bauchi-Gombe kan hanyar komawa Yola jihar Adamawa.

Malamin na Islama ya zaiyana marigayin da cewa mai kwazo ne, mai haba-haba da jama’a da kuma tsayin daka kan aikin sa na wakilin kafar yada labaru ta matakin duniya.

Malamin  ya tuno huldar su ta tsawon shekaru kuma  da yanda marigayin kan kawo ma sa ziyara musamman in ya zo gida a Jimeta don nuna zumunci, ‘yan uwantaka da karramawa.

Sheikh Bala Lau wanda ya ce mutuwa na kan dukkan talikai, ya mika ta’aziyya ga iyali, ‘yan uwan marigayin da kuma Muryar Amurka don wannan rashi na mutumin kirki ko kuma a ce haziki da ya yi jarumtaka wajen aiki a daidai lokacin da fitinar ta’addanci ta ke kan ganiyar ta a arewa maso gabar.

Imam Bala Lau ya yi addu’ar Allah madaukakin sarki ya yafewa marigayin kurakuren sa ya kuma yi ma sa rahama.

READ ALSO:  An haramta zancen dare a Jigawa

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here