TARAIRAYA MAGANIN RIKICIN GIDAN AURE
[63]:
JAN HANKALI DA NASIHA.
Zan so na k’ark’are, tare da kammala wannan
rubutu da jan hankali da nasihohin da za su
k’ara zamar mana k’arin k’aimi da amfani a
koda yaushe. Har kullum ita nasiha tana
zamarwa da Mumini amfani bisa fad’akarwar
alk’ur’ani mai girma;
ﻓَﺈِﻥَّ ﭐﻟﺬِّﻛْﺮَﻯٰ ﺗَﻨﻔَﻊُ ﭐﻟْﻤُﺆْﻣِﻨِﻴﻦَ . [ﺳﻮﺭﺓ ﺍﻟﺬﺍﺭﻳﺎﺕ : ٥٥ ]
Domin tunatarwa tana amfanar da Muminai.
[Zariyat: 55]
Daga abubuwan da za su k’ara taimakawa
ma’aurata su zauna da junansu lafiya, cikin
mutunci da mutuntaka. To sai su kula da
wad’annan nasihohi kamar haka:
1. Ma’aurata ku fahimci manufar da ta had’aku
ta ibada ce da neman lada. Ba sharholiya da
shagala bace.
2. Ma’aurata ku fahimci aure akan rayuwa ce
ta had’aka da Allah SWT ya tsara, babu mai
iya rayuwa ba tare da mahad’insa ba. Ma’ana
dai, ita mace jin dad’in zamanta sai da miji.
Haka shi ma Namiji sai da Mace.
3. Ma’aurata ku sanya zamantakewar ku ta
zama ta amana, ta yanda babu mai cutar da
d’an uwansa. Dukkan ku ku zama masu
takatsantsan.
4. Ma’aurata ku sanya hak’uri da dauriya a
cikin tsarin zamanku. Bahaushe yana cewa; zo
mu zauna, zo mu sab’a.
5. Ma’aurata ku kullewa Shaid’an k’ofa, kada
ku bari ya zama mai kaiwa da komowa a
tsakaninku. Shigowarsa tsakanin ku ba zai
haifar muku da alheri ba.
6. Ma’aurata ku kula da hak’k’in junanku. Kada
d’aya ya tawayewa ‘Dan uwansa hak’k’insa da
Allah SWT ya d’ora masa. Gazawa ta wannan
b’angaren yana girgije zaman lafiyar
ma’aurata.
7. Ma’aurata ku zama masu gaskiya da
amana. Halaye ne guda biyu da suke tafiya,
kafad’a da kafad’a da junansu. Duk abin da za
ku yi, ku gina shi akan gaskiya, kuma kada ku
ha’inci junanku ta hanyar cin amanar juna ku.
8. Ma’aurata ku zama masu yawan yafewa
junanku dukkan sab’anin da ya shiga tsakanin
ku, ba tare da k’ullatar juna ba. Da barin ajje
damuwa a cikin zuciya, domin yawan tuna
damuwa yana hana zaman lafiyar ma’aurata.
9. Ma’aurata ku zama masu yawan kyautata
zato ga junanku. Kada ku kasa samun
amincewa junanku, k’urilla da bibiya mara
amfani, sartse yake yiwa aure.
10. Ma’aurata ku rinka mutunta junanku. Kada
ku zama masu wulakanta junanku, da yiwa
juna kallon biyu ahu, yin hakan ba mutuncin
ku bane.
11. Ma’aurata ku raba kanku da murd’ad’d’en
hali, ku zama masu sauk’in kai da fahimtar
junanku ba tare da cece – kuce ba.
12. Ma’aurata ku kiyayi yawan jayayya ko
musu da junanku, saboda hakan na da saurin
kawo rikici a tsakanin juna, shi kuwa rikici
tsakanin ma’aurata baya haifar da alheri.
13. Ma’aurata ku kiyaye lafuzan da bakunan ku
ke furtawa, musamman idan aka samu rashin
fahimta a tsakaninku. Kasa kiyaye lafuza kan
janyo a afkawa Iyayen juna ko yin saki cikin
ganganci, yin hakan kuwa bai dace ba.
14. Ma’aurata ku kiyayi k’in d’aukar shawara,
k’in d’aukar shawara ba ya haifar da komai
face da na sani. Nadama ce ta ke biyo bayan
k’in d’aukar shawara.
15. Ma’aurata ku kiyayi sab’awa k’a’idar da
shari’a ta shimfid’a a cikin aure. Domin
sab’awa shari’ar aure, sab’on Allah ne. Allah
zai yi muku hisabi a ranar lahira .
Tabbas ga ma’auratan da suka tsara kansu
akan tsarin da wannan littafi tsara, tun daga
farko, har zuwa karshensa, da yardar Allah
tsohon aure za a tayar masa da komad’arsa.
Shi kuwa sabon aure, zai ginu akan farin ciki
da jin dad’i.
Ina rokon Allah da ya bamu lafiya da zaman
lafiya a dukkan gidajen auren mu. Ina mana
fatan samun amfana da abin da wannan
rubutu ya k’unsa. Inda na yi daidai Allah ya
bani lada, inda nayi kuskure, Allah ya yafe
mini.
Ina mai kammalawa da godiya ga Allah.
Dan Uwanku a musulunci:
Ali Dan Abba.