Home Wasanni Tarihin Riga mai Lamba 7 a Duniya

Tarihin Riga mai Lamba 7 a Duniya

0

Lamba 7 tana daga cikin lambobi mafiya daraja a ƙwallon ƙafa. A Tarihin ƙwallon ƙafa na duniya anyi ƴan wasan ƙwallon kafa da yawa da suka goya riga mai lamba 7, kuma suka taka rawar gani a duniya a fagen ƙwallon ƙafa, za’a a iya cewa ma itace lamba ta 3 a jerin lambabobi masu daraja a ƙwallon ƙafa idan ka cire 10, 9, sai 7.

Ƴan wasan da Sukafi shahara cikin waɗanda suka goya riga mai lamba 7 sune :

 1. Eric Cantona
 2. -Cristiano Ronaldo
 3. Luis Figo
 4. Kenny Dalglish
 5. Raul
 6. George Best
 7. Garrincha
 8. Johann Neeskens
 9. Andriy Shevchenko

A cikin jerin ƴan wasan da suka goya riga mai lamba 7 Cristiano Ronaldo shine ɗan wasan da yafi fice a cikinsu, sannan kuma shine yafi taka rawar gani a fagen ƙwallon ƙafa.

Shin Wacce Rawa Ronaldo Ya Taka a Kwallon Kafa?

Abune mai matuƙar wahala a iya bayyana rawa da nasarori da Ronaldo ya samu a ƙwallon kafa, saidai zanyi duba akan muhimman Tarihi da bajintar da yayi a ƙwallon kafa.

Ronaldo ɗan wasan juventus ne ɗan ƙasar Portugal, ya buga wa a ƙungiyoyin Sporting CP, Manchester United, Real madrid da kuma ƙasar Portugal.

A duniyar Ƙwallon kafa ana yima Ronaldo kallon ɗan wasan gefe da babu kamarsa a duniya, sannan ɗaya daga cikin jerin ƴan wasan ƙwallon kafa ba babu kamarsu a duniya.

A Tarihin ƙwallon ƙafa Cristiano Ronaldo shine ɗan wasa da yafi kowanne ɗaukar hankali a duniya, sannan kuma shine yafi kowanne mutum fans a duniya a wannan ƙarni, sannan shine yafi kowanne mabiya a shafin Facebook da  Instagram.

Kai shafukan jaridu da dama a duniya sun bayyana cewa Ronaldo shine mutumin da yafi kowanne magoya baya a duniya, duk inda ka zagaya a faɗin duniya sunan Ronaldo ya zagaya kunnuwan Al’umma koda ba ma’abota kallon ƙwallon bane shi yasa ake kallon shine mutumin da yafi kowanne shahara a duniya.

READ ALSO:  Coach din Real madrid Zidane ba ya bukatar Bale a Real Madrid cewar sa

Tarihin Nasarorin Cristiano Ronaldo

 • A Tarihin Ronaldo ya lashe kofuna guda 30. Champions League 5, FIFA Club World Cup 4, Premier League 3, UEFA Super Cup 3, LaLiga 2, Copa del Rey 2, English League Cup 2, Spanish Super Cup 2, English Community Shield 2, Serie A  2, Italian Super Cup 1, FA Cup 1, Portuguese Super Cup 1.
 • Ronaldo ya buga wasanni sama da 1,000 a Tarihi, sannan kuma ya jefa kwallaye sama da 700 a official match, sannan ya ciwa ƙasar sa ƙwallaye 101, hakan ne yasa ya zama na biyu a jerin ƴan wasan da Sukafi jefama ƙasarsu kwallo a duniya, sannan shine kan gaba a nahiyar Turai baki ɗaya.
 • Ronaldo shine yazo na biyu a ƴan wasan da Sukafi lashe kofin Champions League a duniya inda ya lashe guda 5 inda sukayi kankan kan da Alfredo Di Stéfano tsohon ɗan wasan Real Madrid, da Alessandro Costacurta tsohon ɗan wasan Acmilan, da  Paolo Maldini, inda Francisco Gento ke matsayin na ɗaya a jerin waɗanda sukafi lashe kofin. Kuma gabaki ɗaya champions league 5 daya ɗauka shine ɗan wasan da yake jan ragamar ƙungiyar.
 • Ronaldo ya lashe lambobin yabo guda 100 daidai, daga cikinsu akwai:
 • Gwarzon ɗan wasan duniya (FIFA Ballon d’Or / Ballon d’Or) sau 5: 2008 , 2013 ,
 • 2014 , 2016 , 2017 .
 • Gwarzon ɗan wasan fifa na duniya (FIFA World Player of the Year) guda 1 : 2008.
 • Gwarzon ɗan wasan fifa na maza (The Best FIFA Men’s Player) guda 2 : 2016 , 2017.
 • Ƙwararren ɗan wasan fifa na shekara (FIFPro World Player of the Year) sau 1 : 2008.
 • Gwarzon ɗan wasan nahiyar Turai (UEFA Best Player in Europe AWARD) Sau 3.: 2014, 2016, 2017
 • UEFA Club Footballer of the Year : 2007–08.
 • UEFA Club Forward of the Year : 2007–08.
 • Matashin dan  ƙwallon kafa da babu kamar sa (FIFPro Special Young Player of the Year) sau 2: 2003–04, 2004–05.
 • Gwarzon ɗan wasan ƙasar Portugal (PFA Portuguese Player of the Year) sau 4 a jere : 2016, 2017, 2018, 2019.
 • European Golden Shoe : 2007–08, 2010–11, 2013–14, 2014–15.
 • ƙwallo mafi kyau a 2009 (FIFA Puskás Award) : 2009.
 • FIFA FIFPro World11 : 2007, 2008, 2009, 2010 , 2011 , 2012 , 2013 , 2014 , 2015 , 2016 ,2017 , 2018 , 2019.
 • UEFA Team of the Year : 2004 , 2007 , 2008 , 2009 , 2010 , 2011 , 2012 , 2013 , 2014 , 2015 , 2016 , 2017 , 2018 , 2019.
 • UEFA Champions League Squad of the Season: 2013–14 , 2014–15 , 2015–16 ,
 • 2016–17 , 2017–18 , 2018–19.
 • UEFA European Championship Team of the Tournament : 2004 , 2012 , 2016.
 • FIFA Club World Cup Golden Ball : 2016.
 • Premier League Player of the Season : 2006–07 , 2007–08.
 • FWA Footballer of the Year : 2006–07 , 2007–08.
 • Premier League Golden Boot :2007–08.
 • La Liga Best Player : 2013–14.
 • La Liga Best Forward : 2013–14.
 • La Liga Most Valuable Player : 2012–13.
 • La Liga Team of the Season : 2013–14,
 • 2014–15 , 2015–16.
 • UEFA La Liga Team of The Season: 2015–16, 2016–17.
READ ALSO:  Tarihin Riga mai lamba 6 a Duniya

FAGEN TARIHI.

 • Shine ɗan wasan da yafi kowanne jefa kwallaye a gasar cin kofin nahiyar zakarun inda ya jefa kwallaye 130,sannan shine yafi kowanne Assists a GASAR Inda yayi guda 40.
 • Ronaldo Shine Dan wasan dayafi kowanne cin penalty a tarihin gasar laliga, inda yaci guda 66 a shekaru 9, a Tarihinsa ya zubar da guda 12 a gasar laliga.
 • Ronaldo ne Dan wasa na farko daya fara jefa kwallaye samada 25 a kakar wasanni 9 na laliga.
 • Ronaldo shine kadai yaci kwallaye sama da 40 a Jere a gasar laliga.
 • Ronaldo ne Dan wasan farko daya taba cin kwallaye samada 30 a kakar wasanni 6 kuma a Jere.
 • Ronaldo ne kadai Dan wasan daya jera shekaru 8 yanayin hatrick samada guda 2 a kowacce kakar wasa ta laliga.
 • Ronaldo ne dan wasa na farko daya taba cin kowacce kungiya da suke buga gasar laliga a shekara 1.
 • Ronaldo ne kadai Dan wasan daya jera wasanni 6 ya saka kwallaye a wasan EL-CLASICO.
 • Ronaldo ne Dan wasan farko daya fara jefa kwallaye 20 a waje a gasar laliga.
 • Ronaldo ne Dan wasan da yafi kowanne cin kwallaye 3 (Hatrick) a gasar laliga inda yayi guda 34.
 • Ronaldo ne Dan wasan daya taba cin kwallaye 15 a wasanni 8 na farko na gasar laliga dukda ya rasa wasa 1 daga ciki.
 • Shine Dan wasa na farko daya taba saka kwallaye 25 a wasanni 15 na farko a gasar laliga.
 • Ronaldo ne kadai Dan wasan daya taba lashe kyaututtuka guda uku a gasar laliga a kakar wasa guda, Gwarzon Dan wasan laliga, gwarzon dan wasan gaba, sannan kwallonsa itace kwallo da tafi kowacce kyau a shekarar 2013/2014.
 • Ronaldo ne Dan wasan da yafi kowanne saurin cin kwallaye 200 a gasar laliga a cikin wasanni 178.
 • Ronaldo ne Dan wasan daya fi kowanne cin kwallaye 3 a kakar wasa guda inda yayi guda 8.
 • Ronaldo Shine Dan wasan dayafi kowanne saurin cima kungiyar sa kwallaye 300 a gasar laliga, sannan shine yafi kowanne parentage a gasar laliga a cikin shekaru 9 daya kwashe a kungiyar.
READ ALSO:  Madrid ta siyar da Requilon ga Tottenham akan kudi Euro Miliyan 30

Wannan itace taƙaitattiyar Nasarar da Ronaldo ya samu a fagen ƙwallon ƙafa, yanzu haka shine ɗan wasan da babu kamarsa a Tarihin Real madrid, kuma shine ɗan wasan nahiyar Turai da babu kamarsa A Tarihi, sannan ya shiga jerin ƴan wasan da babu kamar su a laliga, sannan yana daga cikin jerin ƴan wasan da babu kamar su a Tarihin ƙwallon ƙafa.

Saidai ni a wajena shine ɗan wasan ƙwallon kafa da babu kamar sa a duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here