TSAKANIN ABDULJABBAR DA SHAIDA NA HUDU, PROF. AHMAD MURTALA…

A zaman kotun da ya gabata ne Abduljabbar ya gatabar da tambayoyi (Cross Examination) ga shaida na hudu.
Tun bayan tashi daga zaman kotu, mutanen Kogo suke ta yada son zuciyarsu akan tambayoyi da amsoshin da suka gudana a tsakanin su. Wannan yasa tun a wancan lokacin na alƙawarta muku cewa zan kawo muku kadan daga cikin tambayoyin da Abduljabbar ya yiwa shaida na hudu.
Kamar yadda na ambata muku a baya, tambayoyin da Abduljabbar ya yiwa shaida na hudun sun kasu kashi Uku:-
A. Wadanda basu da alaka da abinda Prof. ya bada shaida a kai (ko da suna da alaka da case din).
B. Wadanda ma basu da alaka da case din gaba daya.
C. Wadanda Shaida na huɗu yayi magana akan su, kuma suke da alaka da case din.
(Nasan dai kun san cewa idan za’a yiwa shaida tambaya, ana yi masa ne akan iyaka abinda ya faɗa, ba’a yi masa kowacce irin tambaya ko da tana da alaka da case).
Idan kun tuna, a rubutu na na rahoton abubuwan da suka faru a kotu, na fada muku an yi zama na kimanin awanni 7 da rabi, to acikin wadannan awanni 7, kusan awanni 2 ne kawai aka yi su a waɗansu abubuwan, amma duk ragowar sun shafi tambayoyi ne tsakanin Abduljabbar da shaida na hudu. Kun ga kenan rubuce su gaba-daya zai yi matukar wahala. Hakan ne yasa zan zabi kadan daga ciki, musamman waɗanda shaida ya ambata wa kotu, kuma suke da alaka da case, ga kadan daga ciki:-
Abduljabbar: Game da auren dole, ƙwace, da fyaɗe, korewa kaji ina yi ko tabbatarwa?
Shaida: Duk waɗannan din basa cikin hadisan Annabi SAW da ka faɗa.
Abduljabbar: Bayan alkawarin da ka ɗauka akan zaka faɗi gaskiya a shaidar da zaka bayar, kace ba zaka ƙara ba ba zaka rage ba, sai gashi a wancan zaman ka tsallake hadisi na (1365) bakayi maganar sa ba sai a yau.
Shaida: Hadisin da kake magana akan sa, na Anas Bin Malik, na fade shi a wancan zaman, kuma yau ma na fade shi, kuma an rubuta.
Abduljabbar: Nayi tsammanin yau kazo nayi maka tambayoyi ne, ba kazo ka bada shaida ba?
Shaida: Ai yau ma shaidar nazo na bayar tunda ba’a rufe shaida ta ba.
Abduljabbar: A karatun da kayi, ka karanta faɗin Anas (R.A) na cewa “muka zo musu yayin da rana ta hudo”, to yaya zamuyi da hadisin Bukhari na 4197 wanda Anas ɗin yake cewa Annabi SAW ya isa Khaibar da daddare???
Shaida: إِنَّا إِذَا نَزَلْنَا بِسَاحَةِ قَوْمٍ فَسَاءَ صَبَاحُ الْمُنْذَرِينَ aka ce, zaka iya zuwa wani wuri da daddare, shiga kuma ga bari sai da safe, ana nufin kofar shiga Khaibar ne, shiyasa ma aka bayyana cewa ‘gasu sun fito wajen ayyukan su’, wanda hakan yake nuwa cewa an haddace hadisin…
Abduljabbar: A ciki, da akace (أتيناكم) yana nufin a cikin Khaibar ne da rana, ko a wajenta?
Shaida: Shine dai kamar yadda na fada, sun je da daddare, kuma sun shiga da safe.
Abduljabbar: a lafazin, ance (وَأَنَا رَدِيفُ أَبِي طَلْحَةَ), idan na nuna maka riyawa sahihiya a cikin Musnad, Anas yace shi kansa Abu Dalha bashi da abin hawa, Annabi SAW ne ya goya shi a nasa abin hawan, me zaka ce?
Shaida: Ai ba’a haɗa abin da yazo a cikin Bukhari da Muslim, da wanda yazo a wani littafin daban, musamman idan sun ci karo, malamai suna ƙaddamar da wanda yazo a Bukhari da Muslim.
Abduljabbar: Idan kuma cin karon ya zama a cikin Bukharin ne fa?
Shaida: Yadda za’ayi shine, akwai hanyoyi sama da 100 da malamai suka faɗa na yadda za’a iya hada tsakanin ruwayoyi biyu ingantattu ayi aiki da su gaba daya, ko kuma ayi aiki da wadda tafi inganci.
Abduljabbar: Naji dadin wannan maganar, yazo a cikin Bukhari cewa Nana Safiyya ta kasance matar Annabi SAW tun kafin Khaibar da shekara daya, (a hadisi mai lamba 3085) a can kuma an ce a Khaibar ya same ta, me zaka ce?
Shaida: Yadda za’a haɗa tsakanin su shine, za’a duba waɗanda suka ji ruwayar daga Anas, sai a gwada a gani su waye suka fi yawa wajen ruwaito hadisin, da kuma waɗanda suka kawo shi a takaice ko kuma da waɗansu lafuzzan daban…
Da irin wannan hanya malaman hadisi suke tantance waɗanda suka fi kawo riwaya. Saboda wata ka’ida ta malaman hadisi da suke cewa “idan baka tattara hanyoyin hadisi ba, kuskuren cikinsa ba zai bayyana gareka ba” …
Abduljabbar: Kenan idan aka haɗa hanyoyin, aka samu wanda yafi yawan hanyoyi, ya za’ayi da dayan tun da ya inganta?
Shaida: Ana rinjayar da wanda yafi yawan hanyoyi ne, shi kuma ɗayan yana nan a sahihinsa, amma an rinjaye shi ne.
Abduljabbar: idan na fahimce ka, kenan zan iya kudurce ingancin duk biyun, da me cewa Annabi SAW ya auri Safiyya kafin Khaibar da shekara daya, da kuma mai cewa sai a Khaibar ya aure ta?
Shaida: Kai’dar da na fada tana nan a tabbace, amma misalin da ka kawo bai hau kan wannan kai’dar ba.
Abduljabbar: A wancan zaman, kace Safiyya (R.A.) ta gamsu da auren, duk da yake baka faɗi nassi ba, tun da babu a cikin hadisin, to me zaka ce akan abinda malaman sira suka kawo, cikinsu har da Ibnul Qayyum halifan Ibn Taymiyya, cewa ‘Abu Ayyubal ansary ya kwana da takobi zararre a bakin tantin da Annabi SAW ya shiga tare da Safiyya. Sai da yaga Annabi SAW ya fito da safe, sai yayi kabbara, da Annabi SAW ya tambaye shi mai ya faru? Sai yace wa Annabi SAW “a yau ka kashe babanta, ka kashe kawunnanta da duk danginta, kuma ka aure ta ka tare da ita, wallahi naji tsoron kada ta kashe ka”…
Me zaka ce a kan wannan???
Shaida: Bisa ga kai’dar da malaman Hadisi da suke cewa:
وليعلمِ الطالبُ أنَّ السّيَرَا
تَجمَعُ ما صحَّ وما قدْ أُنْكرَا
والقصدُ ذكرُ ما أتى أهلُ السّيَرْ
بهِ وإنْ إسنادُهُ لمْ يُعْتَبَرْ
Wannan ita ce kai’dar da aka fitar, dole sai an duba inganci, balle ma ace abinda aka kawo (a sira din) ya sabawa abinda yazo a Bukhari da Muslim.
Kuma ita da kanta Nana Safiyya a cikin wani Hadisi ta faɗi labarin da kanta cewa Annabi SAW ya aureta, kuma ya sanya ƴancinta a matsayin sadakinta. Hadisin yana cikin Mu’ujamul Kabir…
……………………………….
Waɗannan kaɗan kenan daga cikin muhimman tambayoyin da suka wakana, akwai wasu da yawa, amma yawanci basu da alaka da shaidar da shaida na hudu ya bayar.
Ko a rubutun hannu da nayi a kotu, na rubuce kusan shafi 16 a littafi, a hakan ma don ina takaice rubutun a wasu lokuta. Kun ga kenan rubuce wa gaba daya zai bada wahalar rubuta wa da karantawa.
RADDI: Mutanen Kogo suna ta yada wani rubutu na ha’inci game da tambayoyin da suka gudana tsakanin Abduljabbar da shaida na hudu. Muna fada musu su ji tsoron Allah, bayan duniya akwai lahira, kuma abinda suke yi suna kara cutar da jagoransu ne, idan kuma hanyar da suka zaba kenan, to muje zuwa, wata rana zasu gane abinda muke faɗa musu.
Game da masu yin maganganu akan Prof. Ahmad Murtala kuma, zuwa gobe In Allah ya yarda zan muku bayani akan wanene shi, sai mu gwada mu gani tsakanin sa da Abduljabbar akwai haɗi???
Tabbas duk tambayoyin da Abduljabbar ya yiwa Prof, ya amsa su cikin ilimi da fasaha, domin prof ya fi karfin irin su Abduljabbar guda 1000 wallahi.
Ku jira zuwa gobe idan Allah ya kai mu.
Allah ya kunyata masu yin batanci ga Annabi SAW, Allah ya tozarta masu yada zindiqanci da sunan ilimi, Allah ya yi mana maganin masu kawowa addini ɓaraka da sunan gyara.
Awaisu Al’arabee Fagge
Jibwis Social Media
Kano State.