‘Yan Sandan Kano Sun Gayyaci Tson Kwamishinan Kano Mu’az Magaji Dan Sarauniya.
Daga Zaharaddeen Gandu
’Yan sanda a Jihar Kano sun gayyaci tsohon Kwamishinan Ayyuka a Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje, Injiniya Mu’az Magaji.
Mu’az, wanda Gwamnan ya kora bisa zargin ‘yin murna’ da rasuwar Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, marigayi Abba Kyari, dai ya yi kaurin suna wajen caccakar Gwamnatin Ganduje, kamar yadda Aminiya ta rawaito.
Yana dai yawan sukar salon mulkin Gwamnan, da yadda iyalansa suke shiga harkokin mulkin Jihar kane- kane.
Tsohon Kwamishinan dai ya ce “rundunar ’yan sandan ta kira ni ne ta waya, sannan ta umarce ni da in bayyana a hedkwatarta da ke Kano, don in amsa wasu tambayoyi”.
“Lalle gayyatar ba ta rasa nasaba da yawan sukar lamirin Gwamna Gandujen da nake yi”. Inji shi
Kakakin Rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da gayyatar, inda ya ce sun yi hakan ne bayan wani korafi da aka shigar a kansa.